Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB ta fara sakin sakamakon jarabawar ta 2021

 



Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq olayade, ya bayyana a wajen taron manema labarai a Enugu inda ya ce, "Hukumar su zata fara sakin sakamakon jarabawar UTME ta 2021 daga ranar Laraba 23 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito".


Farfesa Ishaq olayade yace, "basu da wani dalili da zai sa su rike sakamakon jarabawar da dalibai saka kammala, ya kara da cewa ya kamata ace yanzu an saki sakamakon wadanda suka fara yin jarabawar, amman saboda bana Hedkwata hakan bai samu ba, kuma bana son a fara sanar da sakamakon yayin da nake waje".


"Amman da zarar na koma Abuja nayi alkawarin zamu saki dukkanin jarabawar da daliban da suka zana domin bamu da dalilin riƙe ta".


Shugaban na JAMB  Farfesa Ishaq olayade yace, "Tawagarsa taje kudu maso gabas din Najeriya ne domin duba yadda jarabawar ta bana ta ke gudana, sannan kuma sukai ziyara sabuwar jami'ar da ke Jahar Ebonyi.


Shugaban ya bayyana cewar a bana dalibai 1,415,501  ne suka yi rijistar zana jarabawar ta UTME 2021, kuma a halin yanzu mutum 1,122,095 sun kammala, saura 66,111 suka rage.



Zaku iya ajiye mana comment a kasa, mun gode da ziyartar shafin Taskar Marubuta.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.