Sako Zuwa Ga Masu Kushe Kyawun Matar Da Na Aura - Sahabi Jarumi A cikin Shirin Kwana Casa'in.

Sako Zuwa Ga Masu Kushe Kyawun Matar Da Na Aura - Sahabi Jarumi A cikin Shirin Kwana Casa'in Na Arewa24




SUNANA ALIYU HUSSEIN....


Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aibata halittar ta, sun san ni bayan dana zama SAHABI a cikin shirin Kwana Chasa'in, basu sanni a lokacin da nake Aliyu ba....


Alhamdulillah Hassana ta kaunaceni a lokacin da ni ba kowan kowa bane, lokacin da hatta a unguwarmu ba kowa bane yasan dani, don haka ne nima na rike alkawarin ba zan iya rabuwa da Hassana ba, koda kuwa me na zama a wannan duniyar...


Akwai Yan'mata masu yawa da suka nuna kauna gareni a yanzu bayan dana zama SAHABI, to amma anya kuwa Aliyu suke so, kodai Sahabin Kwana Chasa'in suke so...?


Soyayya ta tsakani da Allah Hassana ke yimun, haka nima dai soyayya ta gaskiya nake mata, ni da ita ba kyale kyale muka kalla ba...


Ni Aliyu Hussain ina ci gaba da yiwa Allah godiya sakamakon kyautar Mata Hassana day bani, ina kallon kyawunta kwatankwacin sarauniyar kyau ta duniya, ina addu'ar Allah ya hadani da Matata Hassana a aljana.....






Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.