Anga wasu 'yan majalisa suna bacci yayin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yanke gabatar da kasafin kuɗi na 2022

 An kama wasu 'yan majalisa da kyamarori suna bacci yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke gabatar da kasafin kudin 2022

 



A cikin wani faifan bidiyo kai tsaye da aka watsa, an nuni 'yan majalisa uku suna bacci a bakin aiki a ranar Alhamis, 7 ga Oktoba

 Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudi na naira tiriliyan 16.39 da haɗin gwiwar majalisar dattawan  da na wakilan Najeriya.

Bidiyon kai tsaye da aka watsa a gidan Talabijin na Channels ya dauko lokacin da aka ga 'yan majalisar suna bacci a yayin taron majalisar na ƙasa.

Idan baku manta ba shugaban na Najeriya ya gabatar da kasafin kudin 2022 a zaman haɗin gwiwa na majalisar dattawan da ta wakilan Najeriya.



Ba za a iya tantance ko su wane ne acikin 'yan majalisar ba saboda abin rufe fuska da su ka saka a fuskokinsu.

Hakan na nuna cewa ba su damu da kalaman Shugaba Buhari ba.

Shugaban Majalisar Dattawa ya ba da tabbacin zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021.

 A halin da ake ciki, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya tabbatar wa Buhari da ‘yan Najeriya baki daya cewa majalisar kasa za ta zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021.

Da yake magana yayin gabatar da kasafin kudin da Shugaba Buhari ya yi, shugaban majalisar dattawan ya ce majalisar kasa ta kuduri aniyar tabbatar da ganin an zartar da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 zuwa karshen shekara.


Ahmad Lawan yayin jawabinsa ya ce Majalisar Tarayya ta yi alƙawarin yin aiki don tabbatar da cewa Najeriya ta dawo cikin tsarin kasafin kuɗi na Janairu zuwa Disamba.




Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.